Home General Kabiru Sufi ya zama Dan Adalan masarautar Dambatta

Kabiru Sufi ya zama Dan Adalan masarautar Dambatta

Sarkin Fulanin Dambatta da ke jihar Kano, Alhaji Aminu Bello Sulaiman ya amince da naɗin Dr. Kabiru Sa’id Sufi a matsayin Dan Adalan ƙasar Dambatta.

Sanarwar naɗin na ƙunshe cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Fulanin Dambatta ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin shirye – shirye Dr. Bello Adamu Namura.

Sanarwar ta ce “Bisa dogon nazarin halayenka da kuma la’akari da gudummawarka ga Dambatta, jihar Kano da kasa baki daya, da kuma girmama masarautar Dambatta, Mai girma Sarkin Fulani-Dambatta ya umarci a sanar dakai cewa kana daya gada cikin wadanda ya amince a baka mukamin sarautar DAN ADALA a kasar Dambatta“

“Saboda haka an tsara jadawalin shirye shirye da tsare tsaren bikin nadin, wanda da zajar an gama shirye shiryen bikin nadin sarautar, kwamitin tsare tsaren zasu sanar da kat lokacin da za’ayi bikin nadin da zarar an sa rana”

“A madadin Mai girma Sarkin Fulani, muna tayaka murnar samun warnan sarauta da kuma addu’ar Allah Ya tayaka riko, Ya zama jagora bisa wannan amana da nauyi daya dora maka. Muna kuma fatan za’a bada hadin kai wajen bin umurni da dokokin wannan masarauta”

Dakta Kabiru Sufi babban malami ne a kwalejin share fagen shiga jami’a da ke jihar Kano, mamba ne a ƙungiyoyi da dama a ciki da wajen Najeriya.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp