Home General Dakarun sojojin Nijeriya sun sami Nasarar Fatattakar ‘Yan Bindiga tare da ceto...

Dakarun sojojin Nijeriya sun sami Nasarar Fatattakar ‘Yan Bindiga tare da ceto mutane 30 a Jihar Kaduna

Dakarun sojojin Nijeriya sun sami Nasarar Fatattakar ‘Yan Bindiga tare da ceto mutane 30 a birnin Gwari na jihar kano.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin mataimakin daraktan mai magna da yawun ryndunar sojojin Nijeriya shiyya ta daya.
A ranar Alhamis dakarun rundunar shiyya ta 1 sunyi arangama da ‘yan Bindigar da sukayi garkuwa mutanen a kan hanyar Manini dake karamar hukumar birnin Gwari a jihar kaduna.
Dakarun dake cikin tawagar dake raka tsohon Maj Gen SE Udonwa, wanda suke kan hanyar duba ayyukan shalkwatar dakarun Operation Whirl Punch a Birnin Gwari.
Nan sukayi arangama da ‘yan bindigar, bayan fin karfin su ne suka tsere cikin daji, abinda ya bawa dakarun sojin damar kubutar da mutane 30 da suke tsare dasu tare kwato baburan hawa 2, suka kuma share hanyar ga matafiya.
Sanarwa ta kuma kara da cewa dakarun sojojin sun raka mutanen zuwa Udawa da birnin Gwari don cigaba da tafiyar su.

Babban jami’in horas da ayyuka na tsaro, Manjo Janar SE Udonwa, ya yabawa sojojin bisa kwarewa da juriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp