Home General kotun majistare a jihar Kano ta aike da Alhassan Ado Duguwa...

kotun majistare a jihar Kano ta aike da Alhassan Ado Duguwa zuwa gidan gyaran hali

Wata kotun majistare a jihar Kano ta aike da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Duguwa zuwa gidan yari bayan gurfanar da shi a gaban kotun.
Ana zargin ɗan majalisar da muggan laifuka ciki har da zargin aikata kisan kai da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da hannu a kunna wuta a wani gini wadda tayi sanadiyyar mutuwar wasu mutane tare da raunata wasu.
An gurfanar da shi gaban kotu mai lamba 54 dake No man’s land  tare da wani mutum wanda ake zargi sun haɗa baki wajen aikata kisan kai da tayar da zaune-tsaye a ƙaramar hukumar Tudun wada da ke jihar ranar Asabar da ta gabata.
Alƙalin kotun ya ɗage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Maris domin duba buƙatar yiyuwar bayar da belin ɗan majalisar ko kuma akasin haka.
Bayan fitowa daga kotun ne tashar PRNigeria ta sami zarafin tattaunawa da lauyan gwamnatin jihar kano Bar Lamido Abba Soron Dinki inda ya bayyana cewa yanzu haka za su yi Nazari kafin ranar da koton ta sanya a dawo domin cigaba da sauraren karar.
Shima a nasa bangaren lauyan dake kare wanda ake tuhuma Bar. Abdul Adamu Fagge ya bayyana dalilan da ya sanyasu bukatar kotun ta bayar da belin na Alhasan Ado Doguwa.
Akwai lauyoyin masu tarin yawa dake sanya idanu kan Shari’ar a karkashin Barista Mutari Dandago.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mabiya Addinai Biyu a Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Sabuwar YarjejeniyaAn Kashe Matashi Kan Murfin Tayar Adaidaita Sahu a KanoMutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga Sojoji
X whatsapp