Home Labarai NAPTIP ta kuɓutar da mata 11 da aka yi niyyar safararsu zuwa...

NAPTIP ta kuɓutar da mata 11 da aka yi niyyar safararsu zuwa Libya

Hukumar yaƙi da fataucin bil-Adama a Najeriya NAPTIP ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin da ya kai ga safarar wasu mata ‘yan Najeriya 11 daga ƙasar.

An ceto ‘yan matan ne a makwaɓciyar ƙasar Jamhuriyar Nijar lokacin da wata ƙungiyar masu safarar mutane ke niyyar jigilar su zuwa ƙasar Libya.

Ƴan matan da suka kasance dukkaninsu matasa, an dawo da su gida Najeriya tare da miƙa su ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa NAPTIP reshen Sokoto.

Kwamandan NAPTIP na shiyyar Sokoto, Abubakar Tabra ya shaida wa BBC cewa jami’an hukumar kula da shige da fice ta ƙasa reshen Illela ne suka karɓi ‘yan matan a karshen makon da ya gabata, inda ya ce a yanzu sun soma bincike da nufin kamo waɗanda ake zargi da safarar ƴan matan.

Ya kuma ce ana kuma kokarin bincike don gano ‘yan uwan ƴan matan don sake haɗa su da iyalansu.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa waɗanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga kudancin Najeriya.

Rahotanni sun ce an sace musu wayoyinsu da kayayyakinsu a cikin dazukan Jamhuriyar Nijar, inda waɗanda suka yi safararsu suka yi watsi da su, kafin jami’an ‘yan sandan Nijar ɗin su kuɓutar da su tare da miƙa su ga jami’an shige da fice na Najeriya da ke kan iyaka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp