Home Labarai INEC ta sanar da ranar sake zabe a Kebbi da Adamawa

INEC ta sanar da ranar sake zabe a Kebbi da Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar da za a sake gudanar da zabukan jihohin Kebbi da Adamawa.

Babban Sakataren Yada Labarai na INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi ne, ya bayyana hakan a birnin Abuja.

Ya ce za a gudanar da zabukan gwamnoni da na wasu ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a rana guda.

Yayin taron da ta gudanar a ranar Litinin, INEC ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkanin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ranar Asabar, 15 ga Afrilu, 2023,” in ji Oyekanmi.Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakken bayani kan yadda zaben zai gudana a hukumance.

Rahotanni sun nuna cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi na ranar 18 ga watan Maris, an soke zabukan wasu mazabun, abin da ya sanya INEC ayyana sakamakon wasu jihohin a matsayin wadanda ba su kammala ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp