Home Labarai Sama da mutane 100 sun mutu cikin sa’o’i 48 a hare-haren jihar...

Sama da mutane 100 sun mutu cikin sa’o’i 48 a hare-haren jihar Plateau

Wasu bayanai na nuna cewa cikin sa’o’I 48 hare-haren ‘yan ta’adda ya hallaka mutanen da yawansu ya haura 100 a wasu sassa na jihar Pilato dai dai lokacin da gwamnatin jihar ta sanya dokar takaita walwalar jama’a a yankunan da hare-haren ke faruwa.

Dan Majalisar tarayya da ke wakiltar Mangu da Bokkos Solomon Maren yayin jawabinsa gaban zaman zauren majalisar ranar laraba, ya ce mahara na ci gaba da kai hare-hare kan kauyuka tare da kisan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Mr Maren, ya bayyana cewa hare-haren sun fi tsananta a yankin da ya ke wakilta a jihar ta Pulato da ke tsakiyar Najeriya wanda ke nuna bukatar daukar mataki lura da yadda mutanen kauyukan da ake kai hare-haren ke rayuwa cike da fargaba.

Dan Majalisar ya bayyana cewa cikin sa’o’I 48 sai da hare-haren ya kashe mutane fiye da 100 wanda ke nuna mutuwar mutanen da yawansu yah aura 200 a makamantan hare-haren cikin watanni 2 da suka gabata.

A cewar Mr Maren maharan na kone gidaje da gonaki har ma da shagunan da ake adana amfanin gona yana mai kakkausar suka ga matakan da gwamnati ke dauka a kokarin yaki da matsalar tsaron da yankuna da dama ke fama da shi a Najeriya.

Matsalar tsaro na ci gaba da ta’azzara a sassan Najeriya musamman yankin arewaci inda ‘yan bindiga ke kai hare-haren ba gaira babu dalili tare da kisan tarin mutane da kuma sace dukiyoyinsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp