Home Labarai Tinubu ya sauke Shugabannin Hukumomi, ma’aikatu da kamfanonin gwamnatin tarayya

Tinubu ya sauke Shugabannin Hukumomi, ma’aikatu da kamfanonin gwamnatin tarayya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da rushe dukkanin shugabannin hukumomi da ma’aikatu, cibiyoyi da kamfanoni mallakin gwamnatin tarayya, ba tare da bata lokaci ba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey a daren ranar Litinin a Abuja.

Sanarwar ta ce, hakan yayi dai-dai da karfin ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa shugaban kasa don amfanin jama’a.

‘’Rushewar ba ta shafi kwamitoci da kuma Majalisun da aka jera a Jadawali na Uku, Sashi na 1, Sashi na 153 (i) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba,’’ in ji sanarwar

Dangane da wannan an umarci shugabannin ma’aikatu, Hukumomi, Cibiyoyi, da Kamfanonin Gwamnatin tarayya da su mika ragamar wuraren da suke ga manyan Sakatarorin ma’aikatun domin su cigaba da kula da wuraren.

Ana kuma umurtar manyan sakatarorin su kai irin wadannan wasikun zuwa ga shugaban kasa ta karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Don haka, dukkan Ma’aikatu su tabbatar da bin wannan umarnin da zai fara aiki daga ranar Juma’a 16 ga watan Yuni, 2023.

An umurci manyan sakatarorin da su sanar da shugabannin hukumomin da abin ya shafa a karkashin kulawar ma’aikatu/Ofisoshinsu domin  su bi umarnin cikin gaggawa.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp