Home Labarai Majalisar jihar kano ta Amince a nada kwamishinoni 16 cikin 19

Majalisar jihar kano ta Amince a nada kwamishinoni 16 cikin 19

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da mutane 19 da gwamnan kano ya tura musu don nada su a mukaman kwamishinoni kuma yan majalisar zartarwa ta jiha .

Idan za’a iya tunawa PRNigeria ta rawaito a ranar Talata ne gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalisar sunayen mutane 19 da yake so majalisar ta tantance don nada su kwamishinoni.

A ranar jiya Laraba majalisar ta fara aikin tantancewa, yanzu da ta tantance mutane 16 tare da amincewa dasu a Alhamis din nan.

Cikin mutane 19 dai akwai mutum biyu da suka tafi aikin hajji wanda hakan yasa ba a tantance su ba sai kuma mataimakin gwamnan Kano wanda aka amince dashi ba tare da ya halarci tantancewar ba.

Shugaban majalisar Alhaji Isma’il Falgore ya ce sun amincewa gwamnan ya nada mutanen ne, bayan da shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Usaini Dala ya gabatar da kuɗirin hakan, daga bisani bayan tattaunawa akan batun aka amince .

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp