INEC ta shigar da karar Hudu Ari gaban kotu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a Najeriya (INEC) ta shigar da tuhume-tuhume shida a gaban kotu, kan dakataccen kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauke da sannun shugaban sashen wayar da kan al’umma na hukumar, Festus Okoye, ta ce an shigar da ƙarar ce a babbar kotun jiha da ke Yola, a jihar Adamawa.

Sanarwar ta kuma tabbatar da samun takardar kammala bincike kan laifukan da suka shafi zabe daga hannun ‘yan sanda, bayan kammala bincike kan laifukan zabe da aka yi a babban zaben na 2023, ciki har da wanda ya shafi Ari.

Sanarwar ta ce, “Kamar yadda sashe na 145 (1) na dokar zabe ta 2022 ya tanadar, laifin da aka aikata a ƙarƙashin dokar za a iya gurfanar da shi a gaban kotun majistare ko kuma babbar kotun jihar da aka aikata laifin, ko kuma babban birnin tarayya, Abuja.

Bayanin ya ƙara da cewa Kotu ta sanya ranar Laraba 12 ga Yulin 2023 don fara shari’ar.

Yunusa-Ari dai ya shiga matsala ne bayan kammala zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar 15 ga Afrilun 2023, lokacin da ya bayyana Aisha Dahiru ‘Binani’ ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben da aka gudanar a yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 21 hours 18 minutes 31 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 22 hours 59 minutes 56 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com