Home Labarai Babbar Kotun tarayya ta dakatar da yunkurin gayyatar tsohon Gwamna Ganduje

Babbar Kotun tarayya ta dakatar da yunkurin gayyatar tsohon Gwamna Ganduje

Babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a A M Liman ta dakatar da hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar da sauran hukumomin tsaro daga gayyata ko kama tsohon Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan na kunshe ne cikin wata dakatarwa ta wucin gadi da kotun tayi har sai ta saurari karar dake gabanta data shafi zargin take hakkin Dan Adam da tsohon Gwamna Ganduje ya shigar.

Kotun dai ta sanya ranar 14 ga watan Yuli a matsayin ranar da zata fara sauraron karar.

Hukumar ta PCACC dai ta aikawa tsohon Gwamnan da takardar gayyata domin amsa tambayoyi kan wani fefan Bidiyo da ake zargin Ganduje na karbar kudaden kasashen waje, duk kuwa da cewa yasha musantawa.

A ranar alhamis data gabata, bayan bullar waccen gayyata, Jam’iyyar APC mai hamayya a Kano ta fitar da wata sanarwa inda take kira ga tsohon Gwamnan da yayi watsi da waccen gayyata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp