Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa baza ta lamunci zubar da Shara da wasu Al’ummar jihar ke yi ba bisa ka’ida ba.
Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai a zagayen gani da ido da yake yi kan yadda aikin kwashe Shara ke cigaba da gudana a wasu sassan jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Dan Zago ya kuma tabbatar da cewa nan gaba kadan gwamnati zata Samar da tsarin da zai Kara jaddada dokar hana zubar da shara barkatai musamman a wuraren da Al’umma ke sake jibgewa sharar bayan gwamnati ta kwashe.
Yace, la’akari da yadda wasu daga cikin al’ummomin da aka kwashe sharar su a kwanakin baya suka sake jibge sharar a wuraren, hakan na nufin dole sai gwamnati ta fito da tsarin da zai karfafa dokar zubar da shara ga al’umma musamman a wuraren da aka tanada domin zubarwa.
Suma wasu daga cikin al’ummomin da aka kwashe sharar dake yankunansu musamman na kan titin Katsina daura da makabartar abbatuwa sun bayyana irin cikakken hadin kan da zasu baiwa gwamnati domin tsaftace Muhallansu da titunansu.
PRNigeria hausa











