Home Labarai Jirgin hirar da Sojin Nijeriya yayi Hadari a Makurdi

Jirgin hirar da Sojin Nijeriya yayi Hadari a Makurdi

Wani jirgin saman horar da sojojin saman Najeriya FT-7NI ya yi hatsari a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a, yayin da ake wani aikin horo.

Daraktan hulda da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojin sama ta Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce matukan jirgi biyu na samun kulawa a asibitin sojojin sama da ke brinin Makurdi.

“An yi sa’a, matukan jirgin biyu da ke cikin jirgin sun tsira daga hatsarin bayan da suka yi nasarar ficewa daga cikin jirgin. Bugu da kari, babu asarar rayuka ko asarar dukiya a inda hatsarin ya faru.

Ya ƙara da cewa a halin da ake ciki, babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Vice Marshal Hassan Abubakar, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin hatsarin nan take.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp