Dakarun sojojin Nijeriya dake bibiyar mayakan da suka tserewa hari a Asaba, sun sami nasarar kame mayakan IPOB dauke da raunikan harbi a jikin su.
Wannan na zuwa ne bayan wani sumame da dakarun sojoji suka kai kan maboyar mayakan na IPOB a ranar asabar,
Ta cikin wata sanarwa da darakta yada labaran rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya sake wallafawa a shafin hukumar na twitter, tace dakarun dake bin sahun mayakan na IPOB sun sake samun nasarar kwato makamai.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Idan za’a iya tunawa dakarun sojojin bataliya ta 63 karkashin shiyya ta 6 ta kai wani sumame a Safiya Asabar 22 ga watan Yulin 2023 a wani gungurmin DAJI dake Asaba.
Dakarun sun sami nasarar kama mutum daya dake dauke da rauni a jikin sa, gami da wasu mukamai, babu ran hawa Hudu, bindigu kirar Double Barrel guns guda hudu, sai alburusan AK 47 guda biyar Magazines, da wasu Albusai na musamman guda 18 masu rai, sai wayoyin hannu guda shifa 6 da Power bank guda 2, da kuma na’urar sadara kira Boafeng Communication Radios guda shifa da waya kira Android, sai Computer kirar HP guda daya da tutocin kungiyar IPOB guda goma sha uku da dai sauran su.
PRNigeria hausa












