Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da hukuncin ladabtarwa ga jagororin Babban Asibitin Gumel da ke Jihar Jigawa.
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar bazata da gwamnan ya kai Babban Asibitin a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya tarar da asibitin cikin mummunan yanayi da kuma rashin bayar da kulawar lafiya ga majinyata yanda ya kamata.
Read Also:
Sanarwar da Mai Magana da Yawun Gwamnan, Hamisu Gumel ya sanyawa hannu, ta ce, Gwamnan ya rushe Hukumar Gudanarwar asibitin tare da ɗauke manyan jami’an asibitin inda aka mayar da su Ma’aikatar Lafiya da ke Dutse domin su jira hukuncin da ya dace da su bayan an kammala bincike.
Jami’an da abun ya shafa sun haɗa da Shugaban Asibitin, Daraktan Kula Bayar da Duba Marassa Lafiya, Daraktan Mulki, Shugaban Sashin Bayar da Magani, Shugaban Sashin Gwaje-gwaje da kuma Mai Kula da Hada-hadar Kuɗi na asibitin.
Cikin laifukan da Gwamna Namadi ya kama ana aikatawa a asibitin akwai, tursasawa marassa lafiya biyan naira 7000 domin a ɗau jinin ƴan’uwansu a ƙarawa majinyatansu, tursasawa majinyata siyan auduga, rashin samar da ruwan famfo duk da gwamnati ta bayar da kuɗin yin hakan, da kuma rashin zuwa aiki a ɓangaren shugabannin asibitin na Gumel.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 5 hours 12 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 6 hours 54 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com