CBN ya musanta sake fasalin kudin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya ya ce ba shi da wani shiri na sake kirkiro sabbin takardun naira a shekara mai zuwa.

Wata sanarwa da daraktan sadarwa na Bankin Najeriya, Isa Abdulmumin ya fitar ranar Talata, ta bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da wani takaitaccen sakon waya da ake yadawa, wanda ke nuna cewa CBN na shirin sake bullo da sabbin takardun naira a shekara ta 2024. Takardar sanarwa ta bayyana cewa sakon ba haka yake ba.

“Mun shiga damuwa game da wannan batu, wanda muka musanta tun ba yanzu ba, amma ga alama yana samun karbuwa da muhawara masu yawa a kan illar irin wannan manufa ga tattalin arzikin Najeriya.

CBN ya ce “Muna son jaddada cewa bayanin da ke cikin wannan sako, ba haka yake ba”. Ya kara da cewa masu wallafa sako a yunkurinsu na jamhuru, sun jirkita rubutun daga wata tsohuwar manufa ta gwamnan CBN na baya a shekara ta 2007, amma sai suke bayyana shi tamkar yanzu ya faru.

Ya dai nanata cewa a yanzu babu wani shiri na sake fasalin takardun kudin kasar.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 22 hours 19 minutes 52 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 1 minute 17 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com