An saki ɗaliba ɗaya cikin biyar da aka sace a jami’ar Dutsin-Ma

Masu garkuwa da mutane sun saki ɗaliba ɗaya daga cikin biyar da aka sace daga jami’ar tarayya ta Dutsen-ma da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan ɗaliban sun kwashe kwana 45 a hannun ƴan bindigar.

Shugaban jami’ar ya tabbatar da kubutar ɗaya daga cikin ɗaliban, sai dai bai fayyace ko an biya kuɗi ba kafin sakin nata.

A ranar 4 ga watan Oktoba ne wasu ƴan fashi suka kutsa ɗakunan kwanan ɗaliban tare da yin awon-gaba da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan sace wasu ɗalibai a Jami’ar Tarayya ta Gusau.

Satar mutane domin neman kuɗin fansa wata matsala ce da ta addabi yankin arewacin Najeriya, inda ƴan fashi kan far wa al’umma a ƙauyuka da makarantu.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 51 minutes 22 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 32 minutes 47 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com