Home Labarai Sojojin Nijeriya Sun kubutar da Muutane 9 a jihar Kaduna.

Sojojin Nijeriya Sun kubutar da Muutane 9 a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin Nijeriya na shiyya ta 1 sun sami nasarar kubutar da mutane 9 wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su tare da kwato makamai a karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

mukaddashin mai magana da yawun rundunar Lt. Col Musa Yahaya ne ya bayyana hakan inda yace mutanen sun shaki iskar ‘yancin ne a ranar 8 ga watan Disamba.

Yahaya ta cikin sanarwar da ya fitar ranar litinin a jihar Kaduna ya ce dakarun da aka girke a Birnin Yero na gudanar da atisaye a kanzaure, in suka sami labarin cewa ‘yan bindiagra sun yi garkuwa da mutane 11 a kauyukan Anguwar Maharba da Dandami.

ya kara da cewa dakarun dake aikin hadin gwiwa da rundunar tsaro ta JTF, sun sami nasarar kai harin kan ‘yan ta’adda a maboyar su.

“dakarun mu sun yi bata kashi da ‘yan bindigar, inda karfin wuta da matsa kaimi daga dakrun ya sanya dole ‘yna ta’addan suka gudu tare da raunikan harbin bindiga a jukkunan su.

“Sojojin sun sami nasarar kubutar da mutane 9 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su, yayin da ‘yan bindigan suka hallaka mutane 2 kafin isar dakarun.”

ya ce sun sami nasara kwato bindiga kirar AK47 da alburusai, da bindiga kirar gida.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp