Home Labarai Sojojin Nijeriya sun kubutar da mutane 19 a jihohin Katsina da Zamfara

Sojojin Nijeriya sun kubutar da mutane 19 a jihohin Katsina da Zamfara

Dakarun sojin Najeriya na rundunar Hadarin Daji sun sami nasarar kai wa ‘yan ta’adda farmaki tare da kubutar da mutum tara da aka yi garkuwa da su, sun kuma gano makamai da albarusai, da babur da na’urorin sadarwa.

A ranar Alhamis, runduna ta takwas ta sojin Najeriya ce ta yi wannan aikin karkashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut, a karamar hukumar Batsari da Safana da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya inda aka kashe ‘yan ta’adda 10 yayin da wasu da dama suka tsere da munanan raunuka.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce ta samu bindiga kirar AK-47, da alburusai da bindigogi kirar gida guda uku da harba-ruga bakwai da sauran da sauran bindigogi masu hatsari da na’urorin sadarwa da wayoyin hannu da kakin soji tare da babura hudu.

Haka kuma sanarwar ta ce a wannan ranar ce dai kuma dakarun soji na rundunar HADARIN DAJI da ke aiki a jihar Zamfara suka kai samame kauyukan Dansadau da Dandalla a karamar hukumar Maru, inda suka kubutar da mutum tara da ake garkuwa da su da suka hadar da mata biyar da jarirai hudu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun gudu ne suka bar mutanen bayan musayar da jami’an tsaro.

Tuni aka sada mutanen da iyalansu a garin Magami kamar yadda sanarwar ta bayyana.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp