Home General ‘Yan Bindiga sun hallaka mutane 10 a jihar Katsina

‘Yan Bindiga sun hallaka mutane 10 a jihar Katsina

Taswirar Katsina
Katsina

Ƴan bindiga sun afkawa kauyen Kukar Babangida da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda suka hallaka dagacin kauyen Magaji Haruna da ɗansa.

manema labarai a kasar sun ruwaito cewa an kuma kashe wasu mutum takwas a harin da aka kai da misalin karfe 10 na dare ranar Laraba.

Har ila yau, wani mazaunin garin ya bayyana cewa an tafi da mata wanda ba a san adadinsu ba zuwa yanzu.

Mazauna garin sun yi imanin cewa akwai manyan shugabannin ƴan bindiga biyu da ke cin karensu babu babbaka a ciki da wajen karamar hukumar ta Jibia.

Ƙauyen Kukar Babangida ya kasance ɗaya daga cikin kauyuka da ke fama da matsalar ƴan bindiga tun bayyanar ayyukansu a faɗin jihar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp