Rahotannin daga Nijeriya na bayyana cewa dakarun rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro, sun lalata wata maboyar masu garkuwa da mutane tare da kuɓutar da mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a yankin ƙaramar hukumar Yorro na jihar Taraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Cikin wata sanarwa da mai riƙon muƙamin daraktan yaɗa labaran rundunar sojin Najeriya ta 6 da ke jihar, Laftanar Oni Olubodunde ya sanya wa hannu, ya ce sojojin sun ƙaddamar da yaƙi da ‘yan bindigar ne tun da suka yawaita kai hare-hare a yankin ƙaramar hukumar.
Ya ƙara da cewa dakarunsu sun yi gumurzu da masu garkuwar a tsaunukan Gampu da na Ban Yorro, bayan musayar wuta tsakanin ɓangarorin ne, sai ‘yan bindigar suka arce inda suka bar mutum huɗu da suka yi garkuwa da su.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin za su ci gaba da aiki a yankin har sai sun tabbatar da kuɓutar da sauran mutanen da ke hannun masu garkuwar.
PRNigeria Hausa












