Home Labarai Kotu ta haramtawa Abba gida gida Rusau a jihar Kano

Kotu ta haramtawa Abba gida gida Rusau a jihar Kano

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar ci gaba da rusa gine-ginen da ke unguwar Salanta wanda tun farko ta sanya musu alama.

A yayin da yake yanke hukunci, Mai shari’a Simon Amobeda, ya bayyana cewa gine-ginen an mallake su ne bisa ka’ida, don haka ba za a iya rushe su ba tare da amincewar masu su ba.

Masu shigar da kara sun garzaya kotu ne a watan Yulin 2023, suna neman ta kare musu hakkinsu na kadarorin da suka mallaka, amma gwamnatin jihar ta sanya musu alamar rugujewa.

 

A lokacin ne kotun ta ba da umarnin wucin gadi da ke hana gwamnatin jihar daukar mataki har sai an yanke hukuncin karshe.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Alhaji Ali Mai kusa da Ali Rabiu Awwalu da Balarabe Sani Salanta da Umar Ibrahim Batayya da Salisu Idris Daneji da Alhaji Ibrahim Sadi da Umar Shittu Sharubutu.

Lauyan masu kara Kabiru Ishaq Kofa ya ce bisa ga hukuncin da kotun ta yanke, “Gwamnatin Kano ko hukumar raya birane ta jihar (KANUPDA), ko wakilansu, har abada an hana su hari ko rushewa ko ma kwace gine-ginen ba tare da amincewar masu su ba”.

Lauyan ya ce wadanda yake karewa sun bi duk matakan shari’a kafin su mallaki kadarorin tun kafin zuwan wannan gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rusa wasu gine-gine da ake zargin mallakarsu ba bisa ka’ida ba ne kwanaki kadan bayan hawansa mulki.

Gwamnan ya zargi gwamnatin da ta gabata da bayar da filaye ga wasu ’yan baranda da kuma sayar da wasu filaye na makarantun gwamnati da makabartu da masallatai ba tare da bin ka’ida ba.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp