Home Labarai ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 60 a jihar...

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 60 a jihar Kaduna

‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun yi garkuwa da mutam 61 a kauyen Buda dake karamar hukumar Kajuru, a jihar Kaduna dake ARewa maso yammacin Nijeriya.

jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ‘yan bindiga sun shiga garin ne da misalin karfe 11:45 na daren ranar litinin inda suka yi garkuwa da mutane.

kawo yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar basu ce komai ba kan lamarin, sai dai mazauna kauyen sun bayyanawa jaridar yadda lamarin ya faru.

wani mazaunin kauyen Dauda Kajuru, yace masu garkuwar da mutane domin karbar kudin fansa sun yiwa garin tsinke inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

“Akwai ‘yan uwa na cikin wadanda suka yi garkuwa da su a jiya, sai dai labarin da muke samu a safiyar nan da ‘yan bindiggar da wadanda aka yi garkuwa da su din sun isa inda suka nufa,” cewar Manyu.

yace tun bayna da aka cire kwamandan rundunar soji da aka fi sani da (Tega) ayyukan ‘yan bindiga ya cigaba da karuwa a kauyukan karamar hukumar Kajuru.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
ICPC za ta ci gaba da binciken shugaban NMDPRA duk da Dangote ya janye ƙorafinsaKu daina kirana da na janye takarar shugabancin kasa a shekarar 2027Ƴansanda sun ɗauke makeken bam ɗin da aka gani a jihar NejaSojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga tare da ceto wasu da aka sace a BornoNan gaba za ku ga Amfanin dokar haraji -TinubuAmurka ta fara kai harin soji Arewacin NijeriyaSojoji sun daƙile yunƙurin harin ƴanbidiga a BornoGwamnatin Nijeriya ta yi watsi da kudirin hukuncin kisa ga masu garkuwaADC ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar harajiGwamnati Nijeriya ta haramta fitar da itace zuwa ƙasashen wajeTinubu ya maye gurbin Engr Farouk daga shugabancin hukumar NMDPRAICPC ta ce zata binciki shugaban hukumar NMDPRAZa mu ci gaba da kamen masu bakin gilashin mota - Yan sandaMajalisa ta amince da naɗin sabbin jakadun da Tinubu ya gabatarShugaban Najeriya zai iya dakatar da gwamna - Kotun Ƙoli
X whatsapp