Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su sauya halayen su a kan kasar tasu.
Shugaban dai na magana ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga majalisar dokokin ƙasar waɗanda suka kai masa ziyarar barka da sallah.
Tinubu ya ce “lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su sauya hali da tunaninsu ga Najeriya domin ciyar da ƙasar gaba”.
“Yan ƙasa da ke yawon neman wayar lantarki domin su cire da tuge titin dogo da dai sauran ayyukan ɓaagari, E, na amince akwai talauci, akwai wahalhalu. Amma ba mu kaɗai ne mutanen da muke shan wahala ba. Dole ne mu tunkari kalubalen da ke gabanmu.” In ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa “akwai bukatar wasu ƴan ƙasar su sauya tunaninsu su kuma zama masu taimakawa wajen warware ƙalubalen da tattalin arziƙin ƙasar ke fuskanta. Saboda haka akwai buƙatar daina fasaƙwauri da cin dunduniyar tattalin arziƙin.”
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 43 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 24 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com