Dakarun sojojin Nijeriya sun sami nasarar kubutar da Mata 7 da kananan yara 9 daga hannun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar da wallafa a shafin ta X a ranar juma’a, inda ta ce bayan wasu sumame da dakarun sojin hadin gwiwa da jami’an Vigilanti suka kai kan maboyar ‘yan ta’addana sun sami nasarar kubutar da mutanen a karamar Gwoza dake jihar Borno.
Sanarwar tace dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addana ne a yankunan Pulka da Ashagashiya, inda suka hallaka wasu, wasu kuma sun tsre da raunikan harbi a jukkunansu.
Haka kuma rundunar ta ce dakarunta sun kai sumame yankin Komala dake jihar Borno, in da suka hallaka dan ta’adda guda daya tare da kwato makamai masu tarin yawa.
PRNigeria Hausa











