Hukumar dake dakile yaduwar cuttukka ta Nijeriya NCDC tace bata da wadatacciyar Allurar ragakafin cutar kwalara.
Daraktan hukumar Dr. Jide Idris ne ya bayyana hakan, inda yace kasar ta bayar da sallahun allurar ga hukumomin dake da alhakin sayar da ita a duniya da masu bayar da tallafinta, duk da cewa bai bayyana ranar da allurar zata iso ba.
Read Also:
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin ke bayyana yadda mutane 40 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ta kwalara a kasar nan.
Dr. Jide ya bukaci al’ummar kasar nan da su yi amfani da allurer rigakafin da wasu matakan kariya daga kamuwa da cutar ta kwalara.
Cutar kwalara dai na guda cikin cututtukan da ake daukar su ta hanyar shan ruwa ko abinci maras tsafta, wanda takan kai ga hallaka mutun bayan kamuwa da ita.
Bincike dai ya nuna cewa a cikin shekaru hudu da suka gabata cutar ta hallaka mutane 4,364 yayin da aka zargi mutane 139,730 da suka kamu da cutar a kasar nan.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 3 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 44 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com