Home DUNIYA Maitamakin shugaban hukumar Kwastom ya mutu a zauren majalisar wakilai

Maitamakin shugaban hukumar Kwastom ya mutu a zauren majalisar wakilai

Rahoyanin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mataimakin Shugaban hukumar hana fasa kwari ta Kasa dake lura da harkokin kudi da gudanarwa Essien Etop Andrew ya yanke jiki ya fadi a gaban zauren Majalisar wakilan Nijeriya.

A yayin da yake amsa tambayoyin a gaban ‘yan majalisar wakilan Andrew ya sarke, wannan ne ya sanya shi faduwa kasa magashiyyan.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa masu bayar da agajin gaggawa na majalisar sun garzaya da shi asibiti amma abin yaci tura ya kai ga  mutuwar sa.

Ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun majalisar wakilan Akin Rotimi, ya fitar ta ce majalisar zata bayar da gudunmawar don ganin an fahimci lamari da abinda ke kewaye da shi ga dukkanin masu ruwa da tsaki.

Haka kuma ta ce kakakin majalisar Tajuddeen Abbas, ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalai da hukumar ta NCS, yace majalisar ta damu matuka da mutuwar jami’an

Bamidele Salam wanda shike jagorantar Kwamitin dake bincike ya ce kwamitin ya dage zaman zuwa mako guda domin girmama marigayin.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp