Home DUNIYA Zanga-Zaga -EFCC ta girke Jami’an Tsaro a Ofishinta dake jihar Legas

Zanga-Zaga -EFCC ta girke Jami’an Tsaro a Ofishinta dake jihar Legas

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arziki kasa ta’annati ta EFCC ta girke jami’an tsaro a bakin ofishinta na jihar legas bisa zargin gudanar da zanga – zanga kan hukumar.

jaridar Emergency Digest ta ruwaito cewa an hangi wasu dakarun kai daukin gaggawa a bakin kofar shiga hukumar take yaki da masu zagon kasar ga tattalin arziki, cikin su kuwa har da jami’an tsaro DSS wadanda suka rufe dukkan hanyoyin shiga ofishin dake hanyar Awolowo dake yankin Ikoyi a jihar.

wannan dai na zuwa ne bayan hukumar ta fallasa wani shiri na wasu gungun mutane dake shirin gudanar da zanga-zanga a kanta.

A ranar Alhamis din data gabata mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale, yace bayanan sirri sun tabbatar musu da cewa an shirya gudanar da zanga – zanga kan hukumar wanda kuma tsohon Gwamnan jihar da wasu tsuffin minitoci suke da alhakin hadata kan hukumar ta EFCC.

wani mai anfani da shafin X #PidomNigeria shine ya fara yada wani sako ta cikin wata takar dar sanarwa wanda ya yi mata adreshi zuwa ga shugaban hukumar, Ola Olukoyode a shafin dake bukatar matasa su fito ayi zanga zanga  a cikin dare 4 ga watan Yunin 2023.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp