Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya sabon firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer, murnar kama aiki, bayan nasarar da jam’iyyarsa ta yi a zaɓen ƙasar.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce a matsayin Tinubu na tsohon jigon adawa a Najeriya, ya san yadda sabon firaministan ke da ƙwarin gwiwa kan sabon aikin da ya kama.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
”Shekarun da ya kwashe yana jagorantar jam’iyyar hamayya sun ba shi damar sake shiryawa domin sake karɓar iko”, in ji Tinubu.
Shugaban na Najeriya ya ce yadda jam’iyyar ta yi shirin ta kuma sake karɓar mulki bayan shekara 14 ya nuna yadda mista Starmer ke da kyawawan halaye da ɗabi’u na shugabanci.
Shugaba Tinubu ya kuma ce a shirye Najeriya take don yin aiki tare da sabon firaministan don ƙara yauƙaƙa danƙon zumunci da ƙarfafa dimokraɗiyya da kasuwanci da ci gaba tsakanin ƙasashen biyu.
PRNigeria hausa












