Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta sami nasarar kama wasu ‘yan bindiga biyu a jihar Taraba da ke tsakiyar ƙasar tare da ƙwace babura daga hannunsu.
Wata sanarwa da mataimakin kakakin runudunar, Kanal Oni Olubodunde, ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ne suka yi nasarar kama mutanen da ba ta bayyana sunansu ba a ranar Alhamis.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“Samamen da dakaru suka kai bayan tattara bayanan sirri a ƙauyen Geshi na ƙaramar hukumar Donga a jihar Taraba ya yi sanadiyyar ƙwato babur biyu da ‘yanta’addan ke amfani da su,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa an samu bayanan sirrin ne bayan wasu mahara sun kai hari, inda dakaru suka ɗunguma zuwa Geshi kuma suka fara musayar wuta da su “abin da ya sa suka tsere zuwa cikin daji”.
“Yanzu haka ‘yanta’addan na hannunmu domin gudanar da bincike.”
PRNigeria Hausa











