Home General Atiku ya zargi Tinubu da jefa Nijeriya cikin tsaka mai wuya

Atiku ya zargi Tinubu da jefa Nijeriya cikin tsaka mai wuya

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa halin yunwa da ake ciki a Nijeriya manufofin gwamnatin APC karkashin jagorancin Tinubu ne su ka haifar da shi babu gaira babu dalili.

Wannan na cikin wata sanarwa da Alhaji Atiku Abubakar ya fitar kuma aka raba ga manema labarai a Nijeriya, wadda ta dora alhakin yanayin komajin rayuwa da Al’ummar kasar ke ciki na tsadar kayan masarufi kan kudirin shugaba Tinubu.

Atiku ya ce rashin samar da matsaya kan mafi karancin albashi da zai yi dai-dai da yanayin rayuwar da ake ciki, zai zama mummunar barazana ga rayuwar ma’aikata da iyalen su a matakan gwamnatocin tarayya, jiha da kananan hukumomin kasar.

“Tun bayan da gwamnatin Tinubu ta janye tallafin man fetur ba zato ba tsammani ba kuma tanadi, da karya darajar Naira wanda shi ma ba tare da lakari da yanayin  tattalin arzikin kasar da ya dogara kachokan a kan shigo da abubuwan masarufi sarrafafu ko wanda za a sarrafa ba, rayuwar yan kasa ya shiga ma wuyacin hali”. A cewar Atiku Abubakar.

A yanzu shugaba Tinubu na shirin ciwo bashin dala biliyan 2 kari akan dala kusan biliyan 3 da rabi, wanda ba a san manufar cin bashin ba, inda zargi yai kwari cewar bashin na tabbatar da walwalar fadar gwamnatin tarayya ne da manyan jami’an gwamnatin.

Jagoran yan hamayyar ya ce Wannan mummunan bashin zai kara yawan bashin da ake bin kasar zuwa kusan kimanin dalar amurka billiyan 100 wannan zai kara ma gembo gishiri wajen ta’azzara mummunan halin da jama’a ke ciki. Wannan ba karamin bakin labari ba ne.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp