Direbobi a kan babbar hanyar Keffi zuwa Abuja a ranar Litinin sun shiga tsaka mai wuya bayan da sojoji suka tare babbar hanyar domin gudanar da bincike kan motocin da suka nufi Abuja, babban birnin Najeriya.
Sojojin sun dasa shingen bincike a barikin sojoji na Sani Abacha kafin shataletalen AYA.
Jami’an tsaro dai ba su bayar da wata sanarwa ba kafin toshe titin lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa har zuwa gadar Nyanya, sama da kilomita 12 daga wurin binciken motocin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Jaridar Emergency Digest ta ruwaito cewa ma’aikata da masu tireda da ke aiki a Abuja, suna zaune a wajen tsakiyar birnin a wurare kamar Nyanya da Karu da Maraba da Masaka.
Bayan shafe tsawon sa’oi a wuri ɗaya – babu gaba, babu baya, akasarinsu daga bisani sun yanke shawarar komawa gida.
Wasu matasa a Najeriya na shirya zanga-zangar gama-gari daga 1 ga watan Agusta saboda tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.
PRNigeria Hausa











