Home General NCC ta bayar da Umarnin bude layukan da aka rufe a Nijeriya

NCC ta bayar da Umarnin bude layukan da aka rufe a Nijeriya

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya ta umarci kamfanonin sadarwa da su gaggauta buɗe layukan wayoyin da aka rufe saboda rashin haɗa layukan da lambar ɗan ƙasa ta NIN.

Darakta yaɗa labarai na hukumar, Reuben Muoka ne ya bayyana haka ranar Litinin, ta cikin wata sanarwa da NCC ta fitar, ya ce abokanan hulɗar kamfanonin ba sa iya amfani da layukan nasu saboda sun gaza haɗa lambobinsu na NIN da layukan wayoyinsu.

Sanarwar ta ce a ƙarshen makon nan ne, masu amfani da layukan sadarwa suka fuskanci ƙalubale wajen amfani da layukan wayoyinsu saboda rashin haɗa lambobinsu na NIN da layukansu.

“Hakan ya sa an toshe layuka da dama bisa dokoki da ƙa’idojin jaɗa NIN da layukan waya.” in ji sanarwar.

Tun Disambar 2023, hukumar ta NCC ta ke nazari kan wa’adin da aka ɗiba na haɗa NIN da layukan waya, an saka 15 ga watan Afrilu a matsayin wa’adin rufe layukan da ba a haɗa su da lambar NIN ba.

An kuma sake tsawaita wa’adin zuwa 31 ga Yulin 2024 domin bai wa kwastamomi dama su miƙa lambobinsu na NIN domin a tantance.

Sai dai duk da tswaita wa’adin, wasu layukan ba a haɗa su da NIN ba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp