Home Labarai Ana fargabar ‘yan Sanda sun harbi masu Zanga Zanga a Kano

Ana fargabar ‘yan Sanda sun harbi masu Zanga Zanga a Kano

Masu zanga zanga a jihar Kano sun zargi jami’an tsaro da harbi kan masu mutum biyu a cikin su.

Ta cikin wata ganawa da PRNigeria ta yi da guda cikin masu zanga zangar kwamared Aliyu D. yace sun fito zanga-zangar ta lumana amma wasu cikin jami’an ‘yan sandan dake aiki domin samar da tsaro suka fara harba musu hayaki mai saka hawaye inda daga bisani kuma suka fara harbin su da bindiga.

Aliyu yace muddin aka cigaba da tafiya a haka bau dalilin da saka su koma gida sai gwamnati tayi musu abinda ya kamata, na dawo da tallafin man fetur da magance tsadar rayuwar a fadin Nijeriya.

Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin Najeriya, dubban matasa a jihar Kano sai kara fitowa suke daga unguwanni suna taruwa a kan titin gidan gwamnati.

matasan rike da alluna suna ta furta kalmomin “Ba ma yi” wasu matasan na komawa gida suna sake shiri.

Ana fargabar an harbi mutum uku cikin masu zanga-zangar, Jami’an tsaro kuma a wasu wuraren sun zama yan kallo sannan sun janye motocin su ƙanana.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp