Home Labarai Tinubu zai yiwa ‘yan Nijeriya jawabi kan Zanga-Zanga

Tinubu zai yiwa ‘yan Nijeriya jawabi kan Zanga-Zanga

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai yi jawabi ga Al’ummar kasar a ranar lahadi 4 ga watan agustan shekarar 2024 da muke ciki, wandake matsayin rana ta hudu da shiga zanga-zangar gama gari

Wannan dai na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimakawa shugaban na musamman kan harkokin yada labara Chief Ajuri Ngelale, wadda tace shugabn zai yi jawabin da karfe 7 na safiyar lahadi.

Za dai a saka hirar kai tsaye a kafafen yada labarai na gwamnatin tarayya da suka hadar da tv da radio, da suka hadar da  NTA da gamayyar rukunin gidajen radio na tarayya wato FRCN.

Wannan dai na zuwa ne bayan da aka shiga rana ta uku da fara gudanar da zanga-zangar nuna halin da ake ciki na matsin rayuwa da talauci a kasar nan.

Zanga-zanagr dai na neman barin baya da kura, inda ta haifar da asarar rayuka kamar yada kungiyar Amnesty international ta bayyana a cikin rahoton ta.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp