Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da shirinta na sayar wa da ma’aikatan gwamnati buhun shinkafa mai nauyin kilogram 50 ko mai kwano 17, da ta sanar a baya a kan farashi mai rahusa – naira dubu 40.
Ma’aikatar ayyuka na musamman ce ta sanar da haka a wata takarda da ta fitar, ɗauke da sa hannun darektar kula da harkokin jama’a, Aderonke Jaiyesimi, mai kwanan wata, 2 ga watan Agustan 2024.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sai dai takardar ba ta yi bayani kan dalilin da ya sa aka dakatar da shirin ba, ko ma an soke shi ne gabaɗaya ko kuma zuwa wani lokaci aka ɗage shi.
A shirin da aka sanar tun farko, a ranar 1 ga watan Agusta, 2024 ta wata takarda dama’aikatar da fitar, an buƙaci ma’aikatan gwamnati da ke son sayen shinkafar da su je shafin intanet na ofishin shugaban ma’aikata na tarayya su cike wata takarda.












