Karamin ministan gidaje da raya birane na Nigeria Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana bakin kokarinsa wajen gyara matsalolin kasar.
Ministan ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar APC 4G Forum na Kano da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishin sa.
Ya bayyana cewa a halin yanzu shugaban kasar ya kaddamar da ayyuka da dama wadanda aka samar da su da niyya magance matsalolin da ke addabar al’umma.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Minista Gwarzo ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar APC 4G Forum na Kano da su tabbatar da hadin kan jam’iyyar tare da bayar da gagarumar gudunmuwa don samun nasarar Shugaba Bola Ahmad Tinubu a yunkurinsa na sake dawo da kasar nan kan saiti.
Ya kuma shawarci kungiyar da ta hada kan dukkan ‘ya’yan jam’iyyar karkashin inuwa daya domin gujewa maimaita kurakuran da aka yi a baya. Ya kara da cewa ya kamata kowa ya tashi tsaye domin tallata gwamnatin Bola Tinubu.
Tun da farko, Shugaban rikon kungiyar APC 4G Forum na Kano, Kwamared Sale Jeli (Sarkin Fadar Karaye) ya bayyana nagartar Ministan, inda ya bayyana shi a matsayin jagora na gari mai kishin kasa, wanda a kodayaushe ya ba da fifiko wajen yi wa al’ummarsa hidima.












