Home General Gwamnan Kano ya bayar da umarnin Rufe Asusun Ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin...

Gwamnan Kano ya bayar da umarnin Rufe Asusun Ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin jihar

Gwamnan ya bayar da umarnin rufe dukkanin asusun ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin aiwatar da tsarin asusun bai daya Wanda Zai tabbatar da Sanin Kudade da Suka Shiga da Kuma fita Daga asusun Gwamnatin Jihar Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin da yake kaddamar da tsarin tattara kudaden haraji da aiwatar da asusun bai daya ajihar Kano wanda hukumar tattara kudaden haraji ta jiha ta aiwatar.

Gwamna Abba wanda ya nuna damuwarsa kan yadda kudaden harajin jihar Kano suke zirarewa ya ce gwamnatin jiha ta aiwatar da tsarin ne domin dakile hanyoyin zirarewar kudi wanda zai bawa gwamnati damar gudanar da ayyukan raya kasa da cigaban al’uma.

Haka Kuma Gwamnan Ya ja hankalin shugabannin hukumomi da ma’aikatalun jiha dasu yi biyayya ga sabon tsarin, yana Mai jadda cewa gwamnatin jiha zata dauki matakin ladabtarwa ga duk Wanda suka ki yin biyya ga tsarin.

Shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta jiha Dr. Zaid Abubakar Yace abin takaici ne yadda jihohin Lagos da River suka yi wa jihar Kano zarra duk da kasancewar Jihar Kano amatsayin cibiyar kasuwanci a kasar nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp