Home General Hukumar gidajen yarin Kano ta musanta zargin rashin bai wa fursunoni wadataccen...

Hukumar gidajen yarin Kano ta musanta zargin rashin bai wa fursunoni wadataccen abinci

Hukumar Kula da Gidajen Yarin Najeriya reshen jihar Kano ta musanta rahotonnin da wasu kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito na rashin bai wa fursunonin da ke ɗaure a gidajen yarin jihar wadataccen abinci.

A baya-baya nan dai an yi ta samun labaran ƙorafe-ƙorafe kan rashin bai wa fursunonin wadataccen abinci a jihar a shafukan sada zumunta.

To sai dai cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen yarin jihar, Musbahu Lawan K/Nasarawa ya fitar ya ce an yaɗa rahotonni ne kawai domin ɓata wa hukumarsu suna.

”Waɗannan rahotonni abin takaici ne, kuma hukumarmu na shaida wa al’umma cewa walwala da jin daɗin fusunoninmu shi ne babban abin da hukumarmu ta sanya a gaba, don haka ne koyaushe hukumarmu ke tabbatar wannan muradi duk kuwa da halin matsin tattalin arziki da ƙarsamu ke ciki”, in ji sanarwar.

Ya kuma ƙara da cewa ba abinci kawai hukumar hukumar ke bai wa fursunonin ba, har ma da ilimantar da su da kuma ba su horon sana’o’in dogaro da kai da za su taimaki rayuwarsu bayan kammala zaman gidan yarin.

A Najeriya ana yawan samun ƙorafe-ƙorafe kan halin da ɗaurarru ke ciki a gidajen yarin ƙasar, kama daga kula da lafiyarsu da abinci da kuma babbar matsalar cunkoson fursunoni a gidajen yarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp