Home General Dalilin da ya sa Ajuri Ngelale Ya ajje mukamin sa

Dalilin da ya sa Ajuri Ngelale Ya ajje mukamin sa

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale, ya tafi hutun sai baba ta gani saboda rashin lafiya ba tare da shiri ba.

Ngelale ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan shawarwari da iyalinsa suka ba shi, saboda wani mummunan yanayi na rashin lafiya da ya ƙara ta’azzara masa.

Ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aikewa Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a yau Asabar.

Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tuntuɓar iyalinsa saboda yanayin rashin lafiyar da ke ƙara tsananta, kuma hakan ya sa dole ya dakatar da aikinsa na Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yada Labarai da sauran mukamansa.

Ngelale ya ƙara da cewa yana fatan dawowa bakin aikinsa idan ya samu waraka, idan kuma yanayi ya bayar da dama, sannan ya roki a bar shi shi da iyalinsa damar samun zaman lafiya a tsawon wannan lokacin.

Wannan hutun yana nufin zai dakatar da aikinsa na mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu na tsawon lokacin da zai ɗebe yana jinyar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba Hatsarin Jirgin Sama na Ondo: Disu Ya Jajantawa NAF, Ya Jaddada Goyon Bayan Ƴan SandaHukumar Kwastam ta Kwace Wiwi ta N3.67bn da Aka Boye a Cikin Motocin da Aka Shigo da su, da Sauran Kayayyaki a Tashar Jirgin Ruwa ta Legas
X whatsapp