Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta daƙile yunƙurin ƴan ta’adda a Jihar Neja daga kai hari a kan kadarorin Hukumar DSS.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa sojojin, da taimakon jirgin Super Tucano na sojojin sama sun yi nasarar kashe wasu ƴan ta’addan da suka kai harin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Majiyar wadda ta nemi a ɓoye sunanta ta ce lamarin ya faru ne a garin Bassa a ƙaramar hukumar Shiroro na jihar.
A cewar majiyar, sojojin sun samu nasara a kan ƴan ta’adda bayan samun bayanan sirri a kan shirinsu na kai harin a kan kayayyakin DSS.
“Nan da nan aka tashi jiragen Super Tucano, inda suka samu nasarar daƙile yunƙurin na ƴan bindigan. Sannan harin jirgin ya kashe aƙalla ƴan bindiga 30,” inji majiyar.












