Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce dala biliyan 49.8 ba ta ɓace ba a zamanin mulkinsa kamar yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Sanusi Lamiɗo Sanusi ya bayyana a 2014.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wajen ƙaddamar da wani littafi a Abuja.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce ba zai yiwu maƙudan kuɗaɗe irin wannan sun ɓace a wata ƙasa, amma kuma ta iya ci gaba da biyan albashi.
“Ina ganin akwai buƙatar in amsa wasu maganganu da ya faɗa a cikin littafin, musamman waɗanda suke da alaƙa da ni.
“Ya ce an cire shi ne saboda fitar da maganar da ya yi a kan ɓacewar kuɗi dala biliyan 49.8 daga lalitar gwamnati. Gaskiya wannan ba haka ba ne. Ba cire shi aka yi ba, dakatar da shi aka yi,” in ji shi.
“Kafin mu gama kuma wa’adinsa ya ƙare, wataƙila da mun dawo da shi. Amma har yanzu ban yarda cewa dala biliyan 49.8 ya ɓace ba.”
Jonathan ya ƙara da cewa bayan binciken ƙwaƙwaf da aka yi, “da rahoton ya fito, dala biliyan 1.48 ne rahoton ya ce ba a tabbatar ba, amma nan ma sai aka buƙaci kamfanin NNPC ya biya kuɗin a asusun gwamnatin tarayya.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 50 minutes 19 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 31 minutes 44 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com