Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tallafawa mutanen da iftila’in fashewar tankar mai ya shafa a garin Majiya dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa da kyautar naira miliya 100.
Gwamnan ya bada tallafin ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya da jaje ga al’ummar jihar Jigawa bisa wannan ibtila’i wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 160 da kuma jikkata al’umma da dama.
Gwamna Abba ya miƙa ta’aziyyarsa a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano tare da fatan Allah ya kare afkuwar hakan a nan gaba.
Read Also:
Har ila yau gwamnan ya ƙara da cewa ibtila’in ba iya al’ummar jihar jigawa kaɗai ya shafa ba, har ma da al’umar jihar Kano, la’akari da dangantakar dake tsakanin jihohin biyu.
Daga nan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suku rigamu gidan gaskiya ya bawa waɗanda suka jikkata lafiya.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Ɗanmoɗi ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ziyarar jaje da ta’aziyyar da ya kaiwa al’ummar jihar, inda ya ce ziyarar zata kara karfafa dangantakar dake tsakanin jihohin biyu.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 1 hour 13 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 2 hours 55 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com