Kotu ta dakatar da gudanar da zaben ƙananan hukumomi a jihar Kano

Babbar kotun tarayya a Najeriya ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kano gudanar da zaben ƙananan hukumomi.

Mai shari’a Simon Ameboda ne ya dakatar da hukumar gudanar da zaben da ake shirin yi a jihar.

A hukuncin da alƙalin kotun ya yanke ya ce naɗin da aka yi na shugabancin hukumar zabe a jihar da sauran shugabbanni ya saba da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, saboda suna ɗauke da katin jamiyyar NNPP.

Alƙalin ya ce naɗin shugabannin hukumar ya saba da sashi na 199(1) da sashi na 200(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa gyara a 1999.

Har wa yau kotun ta ce naɗin ya saba da sashi na 4(b) na dokokin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano.

Kotun tace hukumar zabe a yanzu ba za ta iya gudanar da zabe ba, duba da yadda aka karya ƙa’idojin naɗin shugabannin hukumar.

Kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC kada ta bawa hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano KANSIEC kayan da za ta yi amfani da su wurin gudanar da zabe har sai an bi dukkanin dokoki da ƙa’idoji wurin samar da shugabancin hukumar.

Kafin hukuncin kotun na yau an shirya yin zaben ƙananan hukumomin jihar Kano ne a ranar Asabar mai zuwa.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 27 minutes 58 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 9 minutes 23 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com