Ƙungiyar masu ƙanana da matsakaitan Masana’antu ta Najeriya, wato Nigerian Association of Small Scale Industrialists (NASSI), ta bude hanyar neman rancen Naira Bilyan 75 da Gwamnatin Najeriya ta sahale musu.
Shugaban Kungiyar na kasa Chief Dakta Solomon Daniel Vonfa ne ya sanar da hakan, a yayin wani taron manema Labarai da ya jagoranta a Shelkwatar Kungiyar dake Babban Birnin tarayya Abuja, inda ya ce a yau suka bude shafin domin Mambobin kungiyar dama dukkan al’ummar Najeriya su nema.
Hanyar neman rancen ita ce “https://fgnboimsmeinterventionloan.boi.ng/ ” a inda wadanda zasu nema ta hannun Kungiyar kuma zasu fara yin rijista da kungiyar ta shafin “https://portal.nassi-ng.org/”.
Read Also:
Da yake karin haske, Babban Ma’ajin kungiyar na kasa, Dakta Abubakar Tanko Bala ya ce ga dukkan masu bukatar wannan rance zasu iya nema ta waccan hanya ko kuma su ziyarci Ofishin Kungiyar NASSI mafi kusa da shi.
Kungiyar ta kuma shawarci Mambobin ta dama dukkan al’ummar kasar da suyi amfani da wannan dama, domin bunkasa kasuwancin su dama samar karin kudin shiga ga kasar dama habbaka tattalin arzikin ta.
Taron manema Labaran ya sami halartar masu ruwa da tsakin Kungiyar na sassan Kasar dama tawagar Manyan Jami’an Bankin Masana’antu na Najeriya wato Bank of Industry, karkashin Jagorancin Hajiya Amina Habu.
A ranar 16 ga watan Oktobar nan ne Gwamnatin Najeriya ta amince da bawa mambobin kungiyar rancen Naira Bilyan 75, ta hannun Bankin Masana’antu domin su bunkasa kasuwancin su dama farfado da tattalin arzikin kasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 45 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 26 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com