Kace-Nace ya barke tsakanin IPMAN da Dangote

Ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa IPMAN, ta ce mambobinta ba sa samun loda fetur a matate man fetur ta Dangote duk da cewa sun biya naira biliyan 40 ga kamfanin NNPCL.

Shugaban IPMAN, Abubakar Garima ne bayyana haka a tashar Channels, inda ya ce sun yi mamaki da suka ji Dangote yana cewa dillalan man fetur ba sa zuwa matatarsa sayen mai.

“Idan zai sayar da mai kai-tsaye, za mu saya saboda dole sai mun biya, za a ba mu man. Yanzu haka akwai kuɗinmu naira biliyan 40 a wajen NNPCL, amma ba ma samun kayan. Kwanan nan wasu mambobinmu da NNPCL ta tura matatar Dangote, inda motocinsu suka kwashe kwana huɗu a can ba tare da sun samu man ba.”

A ranar Talata ce dai Alhaji Aliko Dangote ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya bayyana wa manema labarai bayan ganawar cewa yana litar mai sama da miliyan 500 a ajiye, amma dillalan man ba sa sayen fetur ɗin.

A ƙarshe, shugaban IPMAN, ya yi kira ga Dangote da ya duba farashin man matatarsa, sannan ya kwatanta da farashin man na ƙasashen waje. “Shin farashin ya haura na farashin da ake samu daga ƙasashen waje ko ɗaya ne? sannan wane lokaci fetur ke ɗauka kafin ya isa ga dillalin.”

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 45 minutes 39 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 27 minutes 4 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com