Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Borno ta gurfanar da mutum 19 da suka haɗa da wasu ƙananan yara uku a gaban kotu bisa zargin hannunsu a zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta.
An gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Aisha Mohammed Ali a babbar kotun jihar da ke birnin Maiduguri a yau Litinin.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake matsa wa gwamnatin tarayya lamba kan ta janye tuhumar da ake yi wa ƙananan yara da aka kama saboda gudanar da zanga-zangar.
A cewar takardar da aka gabatar a kotun, yaran uku suna tsakanin shekaru 14 zuwa 17.
Gwamnatin jihar Borno ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da cin amanar ƙasa, da kuma amfani da kafafen sada zumunta wajen ɓata sunan gwamnan jihar, da kuma tunzura jama’a a su yi wa gwamnati karan-tsaye.
A cewar masu gabatar da ƙara, yaran suna daga cikin mutum bakwai da suka haɗa baki wajen kafa wata ƙungiya mai suna “Zanga-zanga” ta dandalin sada zumunta na WhatsApp da Tiktok, inda ake zargin sun amince da ɗaukar makamai, wanda ya saɓa wa sashe na 79 na dokar jihar Borno ta 2023.
Kazalika, an tuhumi wasu mutane 11 da laifin ɗaga tutar Rasha a bainar jama’a, amma sun musanta zarge-zargen.
Mai shari’ar ta dage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba, inda ta bayar da umarnin kai yaran wuraren tsare yara masu laifi, yayin da za a ci gaba da tsare manyan cikinsu a gidan yara.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 8 hours 35 minutes 5 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 16 minutes 30 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com