Najeriya ta roƙi Chadi kada ta janye daga rundunar ƙasashe ta yaƙi da Boko Haram

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tura wata tawaga mai ƙarfin gaske zuwa N’Djamena, babban birnin Chadi bayan da Shugaban Chadin ya yi barazanar janye dakarun ƙasarsa daga rundunar haɗaka ta yaƙi da ‘yanta’adda a yankin Sahel.

A jiya Lahadi ne tawagar ta Najeriya ta je N’Djamena, inda a can hedikwatar rundunar (MNJTF), da ta ƙunshi dakarun Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Benin, take.

Shugaba Deby ya yi barazanar janye sojojin ƙasarsa ne bayan da mayaƙan da ake zargi na ƙungiyar Boko Haram ne suka kashe dakarun ƙasarsa 40 a tsibirin Barkaram, da ke yankin tafkin Chadi a ranar 27 ga watan Oktoba.

Saboda wannan barazana ne shugaban na Najeriya ya tura tawagar ƙarƙashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, domin tattauna batun haɗin kan tsaron.

Rahotanni sun ce, bayan gabatar da ta’aziyyar Shugaba Tinubu ga Shugaban na Chadi kan rasa sojojin, tawagar ta tabbatar wa da shugaban na Chadi samun cikakken goyon bayan Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci.

Babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar Christopher Musa, wanda shi ma yake cikin tawagar ya ce ƙudurin sojin ƙasashen biyu zai tabatar da nasarar yaƙi da ‘yanta’adda.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1250 days 2 hours 58 minutes 20 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1232 days 4 hours 39 minutes 45 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com