Home General Mayaƙan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya 5 a wani hari da suka...

Mayaƙan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya 5 a wani hari da suka kai ƙarshen mako

Sojojin Najeriya biyar aka kashe wasu sama da 10 suka samu raunuka, a wani hari da mayakan ƙungiyar masu tada kayar baya suka kai wani sansanin sojoji da ke kusa da iyakar ƙasar da jamhuriyar Nijar.

A cewar wasu jami’an sojoji biyu da suka nemi a sakaya sunansu, sun shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, a ranar Asabar ne maharan da suka fito daga ƙungiyar ISWAP sun kai harin sansanin sojin da ke garin Kareto na jihar Borno.

“Mun rasa sojojinmu 5 a musayar wuta wasu 10 sun samu rauni, 4 daga cikin jami’anmu kuma sun ɓace muna ci gaba da nemansu”.

Haka nan ɗayar majiyar, ta ce ƴan bindigar sun kuma tafi da wasu manyan motocinsu huɗu da ke ɗauke da bindigogin kakkaɓo jiragen sama, tare da kona wasu motoci biyar.

Dama dai a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta ISWAP ta fitar a jiya Lahadi, da aka wallafa a shafin SITE da ke bibiyar harkokin ƙungiyoyin ƴan ta’adda, ta yi iƙirarin kashe sojoji sama da 20 a wani harin ƙunar baƙin wake da taka kai da wata mota, sannan ta kuma ce ta kona wani sansanin soji da motocinsu 14.

Garin Kareto da ke da nisan kilomita 153 daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, nan ne bataliya ta 149 ta sojojin Najeriya da ke yaki da mayaƙan ISWAP da Boko Haram ta ke.

An kuma ɗauki tsawon lokaci mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi na yunkurin kai wa wurin hari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp