Home General Ƴanbindiga sun cinna wa gonaki wuta a jihar Zamfara

Ƴanbindiga sun cinna wa gonaki wuta a jihar Zamfara

Wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun cinna wa gonakin manoma da dama wuta tare da yin garkuwa da mutane da dama a wasu ƙauyukan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya

Maharan sun fara kai harin ne a garin Farin Ruwa da ke ƙaramar hukumar Maru da ke a jihar ta Zamfara, inda suka kone gonakin manoma.

Sun kuma kai irin wannan harin a ƙayukan Wanke da kuma Zargada inda suka ƙone amfanin gona.

Mazauna yankunan da ke iyaka da jihar Kebbi, sun ce ƴanbindigar sun sa sun tafka gagarumar hasarar amfanin gonar da suka noma da ya hada da masara da auduga, da wake da sauran su.

Maharan sun zo ne gungu-gungu tare da cinna wa gonakin masara da wake da dawa wuta, abin da kuma ya haifar da hasara mai ɗimbin yawa.

Sun kuma yi awon gaba da dimbin mutane inda suka ƙona gonaki da dama, kamar yadda wasu daga cikin manoman da suka tafka asarar suka shaida wa BBC.

“Muna cikin ƙunci da wahala, kodayaushe idan ba a kai farmaki ba to za a kashe, akwai matsala.”

Rahotani na cewa garuruwan Wanke da Zargada da Dan Godabe na daga cikin wadanda maharan suka addaba.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce matakin da ‘yan bindigar suka dauka na kone gonaki da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, ya sa suna ganin kansu tamkar ba ƴan Najeriya ba.

Ya kuma yi zargin an kyale maharan na cin karensu babu babbaka, kuma babu abin da za su yi face zura ido ga kangin bautar da maharan suka saka su.

“Mutum ma bai sani ba sai ya je gonarsa ya iske ta bushe, sai mutum ya iske bala’in da ya iske sai dai kawai ya yi Kalmar Shahada,”

Sun kuma yi garkuwa da mutum bakwai bayan sun ƙona mana gonaki,” in ji wani mazauni yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp