Home General Majalisar Dattijai Ta amince da dokar haramta fitar da Masara daga Nijeriya

Majalisar Dattijai Ta amince da dokar haramta fitar da Masara daga Nijeriya

Majalisar DattawaN Nigeriya ta amince da gyaran dokar da ta haramta fitar da tsabar masara (wadda ba a sarrafa ba), inda ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara guda ga waɗanda suka karya wannan doka.

Dokar, wadda ta samo asali daga Majalisar Wakilai, tana nufin hana fitar da masara mai yawa, musamman wadda ta kai ko ta haura ton ɗaya.

Ta kuma tanadi tara mai tsada daidai da kimar kayan da aka fitar ko ɗaurin shekara guda ko kuma haɗa hukuncin biyu ga waɗanda suka keta wannan doka.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele na jam’iyyar APC dake wakiltar alúmmar Ekiti ta tsakiya, yayin gabatar da dokar, ya bayyana muhimmancinta wajen magance matsalar ƙarancin abinci a Najeriya.

“Wannan doka mai sauƙi ce kuma an bi dukkan matakan doka da suka dace wajen nazarinta. Ina roƙon abokan aikina su goyi bayanta,” in ji shi.

Sanata Garba Maidoki (PDP, Kebbi South) ya gabatar da gyara don cire abubuwan da ake sarrafawa daga masara, kamar garin masara da man ganye, domin kare amfanin manoma da masana’antun cikin gida.

Gyaran ya sami amincewa bayan ƙuri’ar jin ra’ayin bakunan ‘yan majalisar.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman, ya ce barin abubuwan da ake sarrafawa daga masara zai taimaka wajen ƙirƙirar ayyukan yi.

“Waɗannan abubuwan suna da matuƙar muhimmanci wajen samar da ayyukan yi. Cire su ya dace da manufofin tattalin arziƙinmu,” in ji Jibrin.

Dokar da aka gyara za ta ci gaba zuwa kwamitin sulhu don daidaita bambance-bambance tsakanin Majalisar Dattawa da ta Wakilai kafin a miƙa ta ga shugaban ƙasa don rattaba hannu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp